Dattawan Arewa sun gana da Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Buhari ya ce, ''Najeriya na bukatar gudummawar kowa da kowa''

Wasu dattawan arewacin Najeriya sun gana da shugaban kasar mai jiran gado, inda suka bayyana damuwarsu kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Dattawan da suka ziyarci Janar Muhammadu Buhari a wata tawaga ta gamayyar kungiyoyi kusan biyar, sun sha al'washin bayar da gudummawarsu ga sabuwar gwamnati don magance matsalolin kasar.

Daya daga cikin 'yan tawagar, Farfesa Ango Abdullahi, ya sheda wa BBC, cewa daman babu wata rarrabuwar kai tsakanin dattawan Arewan.

Ya ce, daman rarrabuwar kan da aka gani a baya, wasu da ya ce, an bai wa kwangilar aikin Shugaba Jonathan ya ci gaba da mulki ne suka kawo ta, kuma yanzu sun yi shiru.

Farfesa Ango, ya ce, Janar Buhari, ya bukace su da su sanar da jama'a irin jan aikin da ke gaban gwamnati mai zuwa ganin halin da kasar ke ciki.

Ya kara da cewa aiki ne ba karami ba, wanda ke bukatar gudummawar kowa da kowa.