Belgium ta dakatar da bai wa Burundi agaji

Hakkin mallakar hoto
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane na ci gaba da gudu daga Burundi.

Kasar Belgium ta dakatar da tallafin da take bai wa Burundi domin gudanar da zaben shugaban kasar da ke tafe bayan an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu adawa da Shugaba Pierre Nkurunziza.

'Yan kasar dai sun tsunduma cikin zanga-zanga ne tun lokacin da Mr Nkurunziza ya yanke shawarar neman shugabancin kasar a karo na uku.

A makon jiya ne masu sanya idanu na Tarayyar Turai suka ce Burundi ba ta cika ka'idodjin gudanar da sahihin zabe ba.

Mr Nkurunziza zai kaddamar da yakin neman zabe ranar Litinin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen da ke gudu daga kasar na karuwa sosai.

Fiye da mutane 15,000 suka gudu daga kasar.

An kashe akalla mutane 19 tun da zanga-zanga ta barke a kasar.