'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane

Mayakan Boko Haram sun hallaka dakarun kasar Kamaru biyu a lokacin wani gumurzu a kan iyakar kasar da Nigeria.

Lamarin ya auku ne a karshen mako a lokacin da dakarun Kamaru ke rangadi a garin Zelevet da ke arewacin kasar.

An kashe 'yan Boko Haram su uku a lokacin arangamar.

A makon da ya gabata ma 'yan Boko Haram sun hallaka mutane 20 a wasu kauyuka da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.

Kasashen Nigeria da Nijar da Kamaru da kuma Chadi sun kafa dakarun hadin gwiwa domin yaki da Boko Haram.