Buhari ba zai gallaza wa kowa ba — APC

Image caption Janar Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo

Jam'iyyar APC a Nigeria ta ce shugaban kasa mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, ba zai gallaza wa kowa ba.

Kakakin jam'iyyar APC, Alhaji Lai Mohammed, a cikin wata sanarwa ya bukaci shugabannin da ke barin gado su sa ransu a inuwa ba za a nunawa kowa bambanci ba.

Sanarwar ta ce "Duk wadanda suka tafka ta'asa a wajen mulki dole ne su wanke kansu."

"Shugaba mai jiran gado yana da mutunci, babu haufi a kai, kuma ya bayyana cewar ba zai ta gudanar da bincike barkatai ba," in ji Lai Muhammed.

Sanarwar na zuwa ne bayan da Shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado ya ce Janar Buhari zai gallaza masa da shi da ministocinsa idan ya karbi mulki.