Shugaba Hollande ya gana da Raul Castro

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Raul Castro da Mista Francois Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya gana da shugaba Raul Castro na Cuba, bayan ya yi kiran a kawo karshen takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar.

A jawabin da ya yi a Havana, Mista Hollande ya ce takunkumin karya tattalin arziki da aka sanya wa Cuba tun a shekarar 1962 ya yi mummunan lahani ga bunkasar Cuba.

Shugaban ya bayyana goyon bayansa wajen ganin an janye takunkumin da aka kakaba wa Cuban.

Mista Hollande ne shugaban Faransa na farko da ya ziyarci kasar Cuba, ya kuma gana da madugun juyin juya halin kasar, Fidel Castro.

Duk da irin takunkumin da aka sanya wa kasar ta Cuba, Faransa da Cuban basu taba yanke huldar diflomasiyya a tsakaninsu ba.