Abin da ya sa ba a kama Shekau ba — Deby

Shugaba Deby da Janar Buhari Hakkin mallakar hoto Buhari Office
Image caption Shugaba Deby da Janar Buhari

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya ce rashin aiki tare tsakanin dakarun Nigeria da na Chadi, shi ya sa aka kasa damke shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.

Shugaban Chadin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja inda suka tattauna cikin sirri.

Mr Deby ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa "Abin takaici ne sojojin Nigeria da na Chadi ba sa aikin hadin gwiwa, kuma shi ne abin da ke kawo tsaiko a yaki da Boko Haram."

Shugaba Deby kuma ya ce ba a kawar da Boko Haram baki daya ba, amma dai an yi musu illa sosai.

Daga bisani Mr Deby ya gana da shugaba mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari inda suka tattauna a kan yadda Nigeria da Chadi za su ci gaba da hada kai wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Dakarun Nigeria da Chadi da Kamaru da kuma Nijar ne ke yaki da kungiyar Boko Haram.