'Duniyar 'yan Ghana masu damfara a intanet'

Farat daya ake gane masu damfarar intanet a Ghana. Samari masu motocin kece raini sun bunkusa kwarai ta yadda har suna da lakanin da ake kiransu da shi. Ana kiransu yaran Sakawa.

David matashi ne mai shekaru 25. Kusan shekaru biyu kenan yana damfarar mutane.

Ya ce: "Na san hakan bai dace ba amma ina samun kudi sosai."

A da can yana kwana ne a kwararo. Sai ya gano yadda abokansa suke samun kudi a shagunan intanet ta hanyar damfarar mutane a yanar-gizo.

Daya daga cikin hanyoyin da suke bi shi ne na yaudarar mutane ta hanyar mayar da kansu mata mazauna Turai ko Asiya ko Amurka da suke neman kawance da maza.

Image caption 'Yan damfara a Ghana suna cewa sune matan da ke jikin hoto ko bidiyo don jawo hankalin wanda tsautsayi ya ritsa da shi

Ya koyi damfarar ba tare da yana da isasshen ilimi ba, ya samu isassun kudin da har ya kama hayar gida ya sayi mota har ma ya saura da rarar kudin kashewa.

Amma ya ce kudin ba sa samuwa cikin sauki.

"Wasu na cewa wannan yana da sauki amma ba sauki ko kadan."

"Dole ka zama mai hakuri da wayo da hanzari, sannan dole a samu yarda tsakaninka da Turawa".

'Yan damfara kamar David(an sakaya sunansa) suna yi kamar su kyawawan mata ne.

Suna sanya muryar mata kana daga bisani sai su gaya wa wadanda suke son yaudara cewa ba za su iya ci gaba da magana ba saboda bututun maganar wayarsu ya lalace, sai dai su yi ta musayar sakonnin kar ta kwana kawai.

Image caption Har fina-finai ake yi da ke nuna halayen samarin Sakawa a Ghana

Da sannu har sai sun gina alakar soyayya da su kafin daga bisani su yi musu romon baka har su aika musu da kudi.

Wadansu har karya suke shara wa mutane cewa sun mallaki arzikin zinare da katako ko man fetur domin su ja ra'ayin mutane su aika musu kudi da zummar musayar za a yi kasuwanci.

An sanya wa kungiyar wadannan madamfara a Ghana suna "Samarin Sakawa ," kuma wannan kalma ce ta hausa wato kamar a ce "a saka wani abu."

Samarin Sakawa sun shahara kwarai a Ghana ta yadda ko daliban makarantar firamare na iya gane su, ta yadda suke gudanar da rayuwarsu cikin tsantsar nuna arziki.

Ana ganinsu a duk daren Asabar a wani waje da ake kira Santa Marie, da ke wajen garin Accra, babban birnin Ghana.

Titunan Ghana cike suke da motoci marasa lasin kamar su Range Rovers da kuma Toyota Camry.

Image caption Ana gane giftawar samarin Sakawa a mota ta yadda suke kure sautin waka a motocinsu

Matasa ne masu sanya matsattsun wandunan jins da hular hana sallah da jefi-jefin zinare, suna kuma saukar da tagogin motarsu kasa tare da kure muryar sautin rediyon motarsu.

Shekaru goma da suka gabata ba a kiran wadannan 'yan damfara da Sakawa a Ghana. A maimakon haka - ana kiransu "yahoo boys", kalmar da yawanci aka fi amfani da ita ga 'yan damfarar Najeriya.

Ghana na daya daga cikin kasashen da aka fi amfani da intanet a Afrika, wanda hakan na daga cikin dalilan da suka sa 'yan damfarar suke cin karensu ba babbaka.

Ana zargin yaran Sakawa na da daurin-gindi sosai a Ghana, shi yasa suke fantamawa son ransu.