Ana korar Fulani daga Ghana

Shugaba John Mahama na Ghana Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba John Mahama na Ghana

Hukumomin jihar Volta a Ghana sun ce sun kaddamar da wani shiri na fidda Fulani makiyaya daga jihar.

A makon jiya ne dai Minista mai kula da jihar,ta ce ba sa bukatar Fulani makiyayan da aka koro daga wasu jihohin kasar su shiga jihar.

Tana mai zargin Fulanin da barna a gonakin jama'a da sauran laifuka.

A karshen makon da ya wuce ne dai sojoji da 'yansanda suka kaddamar da wannan aiki na korar fulanin daga jihar Volta.