China ta kaddamar da makaranta a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dalibai a wata makaranta a Nigeria

An bude wata makarantar Sakandare a jihar Kano wacce a cikinta za a dinga kowayar da harshen Mandarin wanda ake amfani da shi a kasar China.

Gwamnatin jihar Kano ce ta gina makarantar a karamar hukumar Madobi tare da taimakon hukumomin China.

Jakadan China a Nigeria ne ya jagoranci bikin bude makarantar wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnati.

Makarantar wacce za ta kasance ta kwana ce, za ta dinga daukar dalibai daga sassa daban-daban na jihar Kano.

Batun bunkasa ilimi na daga cikin abubuwan da gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin aiwatarwa.