Jirgin yakin Moroko ya bace a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jiragen yakin Moroko guda shida ne suke taimaka wa a hare-haren sama da ake kai wa 'yan Houthi

Kasar Moroko ta ce daya daga cikin jiragen yakinta da ke taimaka wa gamayyar kungiyar kawance da Saudiyya ke jagoranta wajen kai hare-hare kan 'yan tawayen da ke Yemen ya bata.

Jiragen yakin Moroko guda shida ne suke taimaka wa a hare-haren sama da ake kai wa 'yan Houthi da kawayensu.

A ranar Talata ne yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki biyar za ta fara aiki.

Amma har yanzu babu alamar dakatar da kai hare-haren sama kan 'yan Houthi musamman a yankin da suka fi karfi da ke arewacin yankin Saada.

A nasu bangaren 'yan Houthi suna ci gaba da harba rokoki cikin Saudiyya.