'Yan Sudan ta Kudu na cikin mawuyacin hali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutanen da ake fada dominsu a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban daruruwan mutane ne ke zaune ba tare da samun agaji ba a kasar Sudan ta Kudu, bayan janyewar hukumomin ba da agajin jin kai.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ta sa kungiyoyin kasa da kasa suka janye jami'ansu daga jihar Unity ,saboda kazamin fadan da ake gwabzawa.

An bar mutanen babu taimakon abinci da maguguna--bayan da aka samu karancinsa.

Dubban daruruwan mutanen ne dai suka rasa matsugunansu a makon da ya gabata, lokacin da fadan ya rincabe tsakanin dakarun da ke goyon bayan shugaba Salva Kiir, da na jagoran 'yan tawaye, Riek Machar.

Dubun dubatan 'yan Sudan ta Kudu sun rasa muhallansu sakamakon rikicin.