'Yan gudun hijira na bukatar $274m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan Najeriya ke gudun hijira a Kamaru.

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar dinkin duniya ta ce tana bukatar dala miliyan 274 domin tallafa wa 'yan gudun hijira 330,000 na kasashen Jamhuriyar tsakiyar Afrika da Najeriya da ke zaune a Kamaru.

Wadannan 'yan gudun hijira sun tsere daga kasashensu ne sanadiyyar hatsarin da suke fuskanta sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram.

Sai dai daukacin 'yan gudun hijiran da suke zaune a Kamaru ba daga Najeriya da Jamhuriyar tsakiyar Afrika suka fito kawai ba; akwai tsirari da suka fito daga wasu kasashen.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International dai ta ce 'yan boko Haram sun kashe fiye da mutane 13,000 yayin da sama da mutane miliyan uku suka guje daga gidajensu.