Amurka ta ce ba gudunta Saudiyya take ba

Image caption Dangantakar Saudiyya da Amurka na neman sukurkucewa saboda Iran

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi magana da Sarki Salman na Saudiyya bayan shawarar da Sarkin ya yanke ta kin halartar taron kasashen Yankin Gulf a wannan makon.

Fadar White House ta Amurka ta hakikance cewa wannan shawarar da Sarkin ya yanke ba ta kauracewa Amurka ba ce.

Sarki Salman ya ce yana bukatar ya zauna a gida domin sa ido a kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Yemen, inda kawancen sojojin da ke karkashin jagorancin Saudiya suka shafe kusan makonni bakwai suna luguden wuta ta sama.

Shugaba Obama ne dai ya kira wannan taro, domin bai wa kawayen Amurkar na kasashen yankin Gulf wani tabbaci, wadanda hankalinsu bai kwanta ba, game da yarjejeniyar nukiliyar da ake shirin kullawa tare da kasar Iran.

Wakiliyar BBC ta ce babu tantama danganta tsakanin Amurka da kawayenta a kasashen Larabawa ta gamu da cikas, sakamakon manufar Obaman tare da kasar Iran.