Boko Haram:'Nigeria ba ta ba da hadin kai'

Hakkin mallakar hoto Buhari Office
Image caption Janar Muhammadu Buhari ya sha alwashin hada kai da makwabtan Najeriya domin kawar da Boko Haram.

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta bayar da hadin kai a yunkurin da ake yi na murkushe kungiyar Boko Haram.

Shugaban Chadin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja inda suka tattauna cikin sirri.

Mr Deby ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa "Abin takaici ne sojojin Nigeria da na Chadi ba sa aikin hadin gwiwa, kuma shi ne abin da ke kawo tsaiko a yaki da Boko Haram."

Shugaba Deby kuma ya ce ba a kawar da Boko Haram baki daya ba, amma dai an yi musu illa sosai.

Daga bisani Mr Deby ya gana da shugaba mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, inda suka tattauna a kan yadda Nigeria da Chadi za su ci gaba da hada kai wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Dakarun Nigeria da Chadi da Kamaru da kuma Nijar ne ke yaki da kungiyar Boko Haram.