Faduwar gini ta raunata mutane 8 a Kano

Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu

A kalla mutane takwas ne suka samu raunuka yayin da wani gini ya fadi a cikin fadar Sarkin Kano da ke arewacin Najeriya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Magaji Majiya, ya ce ginin ya fadi ne a wani bangare da ake gina sabuwar katanga a cikin fadar mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II a ranar Litinin.

Majiya bai yi karin bayani a kan yanayin raunukan da mutanen suka ji ba, sai dai ya ce tuni aka kai su asibiti.

Fadar Kano dai -- wacce za a iya cewa girmanta ya kai na wani madaidaicin gari -- tana tsakiyar birnin ne.