Marina a Kano na korafi kan kayan China

Image caption Zanga-zangar adawa da kayayyakin China da Marina suka gudnar a Kano

Daruruwan marina sun gudanar da zanga-zanga a Kano sakamakon abin da suka kira yadda kayayyakin da 'yan China ke shigo da su suke kashe musu kasuwa.

Suna korafin cewa mutanen China suna ruguza al'amuransu ta yadda suke kin sayar musu da kayayyakin rini na zamani masu inganci wanda hakan ya sa mutane ke guje wa kayayyakinsu suke sayan na China.

Masana sun yi hasashen cewar fiye da mutane 32,000 za su rasa ayyukansu sakamakon barazanar da kasuwancinsu ke fuskanta daga 'yan China a Nigeria.

A makon da ya gabata ne hukumar fasa kwabri ta Najeriya ta kama wadansu 'yan China hudu saboda kama su da ta yi da laifin fasa kwabrin kayan yin tufafi.

Akwai dubban 'yan China da ke gudanar da kasuwanci a Nigeria da kuma wasu kasashen Afrika.