"Da kyar na sha" - Dan ci ranin Afrika

'Yan ci-rani a Afrika masu tsallake tekun Bahar Rum domin zuwa Turai na fuskantar kalubale iri-iri, ta yadda har wasu ke salwantar da rayuwarsu wasu kuma suke sha da kyar.

Image caption Saliou Ndiye dan ci ranin Afrika da ya yi niyyar zuwa Turai amma hakan sa bai cimma ruwa ba

Saliou Ndiaye wanda yana daya daga cikinsu dan kasar Sinigal ne, ya kuma shaida wa BBC irin wahalhalun da ya fuskanta lokacin da ya niyyaci wannan tafiyar wadda ya shafe watanni bakwai yana yin ta ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.

Ya ce "Na yi niyyar tafiya Turai domin a can an fi samun kudi ba kamar Sinigal ba, da samun aiki ke wahala."

Na yi magana da abokina da ke zaune a Italiya ta Skype ya kuma ce min in bi ta Libya domin zuwa Turai kuma zan kashe kimanin 400, 000 CFA; ya dauke ni tsawon shekaru hudu ina aikin gini domin tara kudin.

Kuma abokina ya shaida min cewa ana shan wahala matuka a hanya.

Ban shaida wa iyayena cewa zan je Turai ba, sau daya dai na taba ce musu ina Agadas.

"Tashin hankali a Sahara"

Da farko na bi ta birnin Bamako na Mali, sai na bi ta biranen Yamai da Agadas na Nijar.

Ana fuskantar kalubale da dama idan an bi ta Libya saboda sai an ratsa ta hamada kuma a nan ne mutane suka fi mutuwa.

An cunkusa mu cikin mota daya, kuma mun yi mako guda a tsakiyar hamada inda har muka rasa abin da za mu ci da ruwan sha.

Da kyar wata motar ta zo ta kwashe mu, ta kai mu garin Sabha na Libya inda a nan kuma 'yan tawaye suka yi garkuwa da mu a matsayin fursunoni.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hamadar Libya da 'yan ci rani ke ratsawa a kokarin su na zuwa Turai

"Yin garkuwa"

'Yan tawayen sun karbi kimanin 200,000 CFA daga wajen kowanne mu. Wanda ya kasa biya sai a ce ya kira 'yan uwansa su biya ko kuma su kulleka.

Ni dai na kasa biya shi ya sa na ci duka a wajensu har tsawon kwanaki hudu. A karshe dai na tsira da kyar .

Na samu aikin yi a garin Sabha har na sake tara kudin zuwa Italiya. Ranar da naso bin jirgin ruwa domin tafiya, a ranar na fara rashin lafiya.

Daga baya na samu labarin wannan jirgin da na so shiga ya yi hatsari kuma ba wanda ya rayu a ciki.

Da farko na so na sake tara kudin tafiya Turai amma daga baya na hakura ganin cewa a Libya ma ina samun kudi sosai.

Na sami kamar CFA miliyan biyu cikin wata hudu.

Wata rana kaddara ta fada mana 'yan sanda suka kama mu suka kwace mana kudadenmu tare da kai mu gidan yari inda mu kai wata uku kana daga bisani a ka mayar da ni Sinigal.

"Mafita"

Ban ji dadin rashin isa ta Turai ba, amma ba zan sake yin wata tafiya ta haramtacciyar hanya ba domin na ga irin hatsarin da ke tattare da hakan.

Akwai bukatar shugabannin Afrika su rufe kan iyakokinsu, saboda yadda mutane ke iya tafiya daga Sinigal da Mali da Burkina Faso da Nijar ba tare da wata matsala ba."