An yi yunkurin juyin mulkin soji a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Nkurunziza na fuskantar matsin lamba a Burundi

Wani Janar a dakarun sojin Burundi ya ce manyan jami'ansu sun yi wa Shugaba Nkurunziza juyin mulki.

Janar Godefroid Niyombareh ya shaida wa manema labarai sun kafa kwamitin ceto kasar domin gudunar da ayyukan gwamnati.

Shugaba Pierre Nkurunziza a yanzu haka yana halartar wani taron koli a Tanzania domin tattauna yadda za a warware batun tazarce a karo na uku da yake shirin yi.

Masu suka na zargin cewar yunkurin ya sabawa kundin tsarin mulkin inda aka shafe kwana da kwanaki ana zanga-zanga a fadin kasar.

Ko a ranar Laraba ma, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga.

Sai dai kakakin fadar shugaban kasa a Burundi ya bayyana matakin sojin a matsayin abin wasa.