An kashe mataimakin shugaban IS

Hakkin mallakar hoto US DEPARTMENT OF STATE
Image caption Amurka na nemansa ruwa ajallo

Ma'aikatar harkokin tsaron Iraki ta ce an hallaka wani mamba na biyu a girman mukami a kungiyar IS masu da'awar kafa kasar Musulunci a wani hari ta sama da Amurka ke jagoranta.

Mai magana da yawun ma'aikatar ya shaidawa BBC cewa an hallaka Abu Alaa al-Afari tare da wasu 'yan kungiyar da dama a Tal Afar da ke arewacin in Iraki.

Ya zuwa yanzu babu wani tabbaci daga Amurka a kan wannan harin.

Mahukuntan kasar ta Iraki sun sha yin irin wannan ikirari a baya, ya kan zama ba shi da tushe daga baya.

Al-Afari dai shi ne wanda aka bayyana ya karbi jagorancin kungiyar ta IS a makonnin baya bayan nan, bayan da aka raunata shugaban ta Abu Bakr al-Baghdadi a wani hari ta sama.