Gobara ta kashe mutane 31 a Philippines

Image caption Gobara ta tashi a a masana'antar yin takalma a Filifins

A kalla mutane 31 ne suka mutu sakamakon tashin gobara a wata masana'antar yin takalma a Manila babban kasar Filifins.

Masu aikin ceto na ci gaba da gano gawarwakin mutane daga hawa na biyu na masana'antar da ke arewa da wajen garin Valenzuela.

Har yanzu dai ba a ga kimanin mutane 30 ba.

Gobarar ta rutsa da ma'aikata da yawa yayin da bakin hayaki ya turnuke ilahirin ginin.

Wasu daga cikin ma'aikatan sun yi kokarin aika wa 'yan uwansu sakon kar-ta-kwana domin su kawo musu agaji, amma daga baya an kasa samun su a wayar.

Har yanzu dai ba a san abin da ya jawo gobarar ba.