Burundi: Shugaba Nkurunziza ya koma gida

Mr Nkurunziza ya sanar da komawarsa Burundi ce a shafin Twitter.

Tun farko an yi barin wuta a Bujumbura babban birnin kasar musamman a tashar gidan radio mallakar gwamnatin.

Sai dai a yanzu al'amura sun lafa yayinda sojoji biyar kuma suka rasa rayukansu.

Mr Nkurunziza na kasar Tanzania lokacin da Manjo janar Godefroid Niyombare, tsohon na hannun damansa yi yunkurin yi masa juyin mulkin a ranar Laraba.

A Ranar 26 ga watan Aprilu aka fara zanga zangar adawa da yunkurin sa na neman tazarce karo na uku a karagar mulki.