Ana fama da yunwa a sansanin 'yan gudun hijira

Image caption Tsofaffi da yara na daga cikin dubban 'yan gudun hijira da ke cikin halin ha'ula'i

'Yan gudun hijira da kuma daukacin al'ummar lardin arewa mai nisa a Kamaru na fuskantar matsalar karancin abinci.

Hukumomin kasa da kasa masu ayyukan jin-kai sun tabbatar da cewa lamarin zai dada munana saboda karancin kudin daukar nauyin 'yan gudun hijirar da ke yankin har na tsawon lokaci.

Hakan ne ya sa suka yi kira ga kasashen duniya da su taimaka domin bai wa jama'ar yankin da bakinsu damar ci gaba da rayuwa.

Babban jami'in hukumar kula da bayar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya reshen Kamaru, Jack Roy, ya ce kashi 19 cikin 100 na yaran da ke wannan yanki na fama da tamowa.

Mr Roy ya kara da cewa "muna bukatar dala miliyan 30 domin samar da abinci ga daukacin 'yan gudun hijirar wannan yanki."

Lardin arewa mai nisa na dauke da dubban 'yan gudun hijira ne a dalilin makwabtakar da ya ke yi da jihar Borno, inda farmakin kungiyar Boko Haram ya dai-dai-ta jama'a.