Yara 350 sun kubuta a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Daruruwan yara ne suka kubuta daga hannun kungiyoyin mayakan sa kai a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Sojojin sa-kai masu dauke da makamai a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun sako yara fiye da 300 wadanda mafiya yawan su 'yan kasa da shekaru 12 ne.

Hakan ya biyo bayan wata yarejejeniya da aka cimma da shugabannin 'yan tawaye wadda asusun kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta jagoranta cewa su saki dukkan yaran da ke wajensu.

An gudanar da shagalin bukukuwa har guda uku a ranar Alhamis, a kusa da garin Bambari yayin da mayakan sa-kai na anti-Balaka da 'yan tawayen Seleka suka sako yara 357.

Tuni UNICEF da abokan huldarta suka fara kokarin samar da hanyoyin daidaita tunanin yaran da kuma mayar da su wajen 'yan uwansu.

Wakilin UNICEF Mohamed Malick Fall, wanda ya halarci shagalin bukukuwan ya ce "Sakin wadannan yara da kungiyoyin suka yi bayan shekaru biyu da aka shafe ana gwabza fada, wani mataki ne na samun zaman lafiya. A yanzu yaki da wahala sun kare kuma yara za su samu rayuwa mai kyau a gaba.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin shugabanni 'yan tawaye na kasar guda 10 a Bangi babban birnin kasar a makon da ya gabata, sakamakon hadin gwiwa tsakanin UNICEF da gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.

.