An kammala taron Kasashen Sahel a Yamai

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

A Jamhuriyar Nijar kungiyar kasashen yankin Sahel ta G5 ta ta kammala taronta na kwana 4 a Yamai babban birnin Nijar.

A bayanin karashe taron kungiyar ta bayyana cewar zuba jari a cikin kasashen domin aiwatar da ayyukan ci gaba mai dorewa na daga cikin hanyoyi mafi inganci da ka iya taimakawa wajen shawo kan matsalar ta'addanci da kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai.

A kan haka ne kuma ta ce kasar Faransa tare da sauran kasashen Turai,sun amince su taimaka wa kasashen kungiyar da kudi da kuma matakan tsaro don dakile ayyukan ta'addancin da kuma kwararar bakin haure.

Kungiyar ta kunshi kasashen Moritaniya da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi .