Dole a sake bincike kan mai — Sarkin Kano

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan ne ya kori Sarki Sanusi daga shugabancin babban bankin Najeriya.

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce rahoton da kamfanin bincike na PricewaterhouseCoopers(PwC) ya fitar game da badakalar da ke kamfanin man fetur na kasar ya nuna cewa NNPC na da hannu dumu-dumu cikin cin hanci a Najeriya.

Sarki Sanusi, wanda shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya kora daga shugabancin Babban bankin kasar bayan ya yi zargin cewa NNPC bai sanya kudin mai $20bn a asusun bankin ba, ya bayyana haka ne a wata wasika da aka wallafa a jaridar Financial Times.

Ya kara da cewa rahoton PwC bai wanke kamfanin man daga zarge-zargen badakala ba, sabanin ikirarin da ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta yi cewa an wanke NNPC daga zarge-zargen.

Shi dai rahoton na PwC ya ce ana cuwa-cuwa sosai wajen biyan kudaden tallafin man fetur da kalanzir.

Kamfanin PwC ya ce a wasu lokutan NNPC na biyan kamfanoni kudin tallafin man fetur sau biyu.

Masu binciken sun ce akwai bukatar a yi wa dokar da ta kafa NNPC garanbawul domin tabbatar da cewa dukkanin kudaden da kasar ke samu daga sayar da danyen mai na shiga asusun gwamnatin tarayya kai-tsaye.

Rahoton na binciken kuma ya bukaci NNPC ya mayar wa gwamnatin Nigeria kusan dala biliyan daya da rabi saboda kin saka wasu kudaden da aka sayar da man fetur a kasar.