Ghana ce koma-baya a ilimin Firamare

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Rashin ingancin ilmin Firamare da na Sakandare kalubale ne ga mahukuntan Ghana

Wani bincike da wata kungiya mai zaman kanta, wato Organisation for Economic Co-operation and Development ta gudanar, ya ce kasashen Asia suke kan gaba wajen samun ilimin firamare da na gaba da firamare mai inganci

Binciken ya nuna cewa Kasar Singapore ita ce ta zo ta farko, a yayin da Amurka kuma ta zama ta ashirin da takwas.

Sai dai binciken ya nuna cewa Ghana ita ce ta zo ta karshe.

Gwamnatin Ghanan ta yi barazanar korar shugabannin makarantu idan har ba su kara kaimi ba a harka koyarwarsu.