An kashe mutane 11 a wani otal a Kabul

Image caption 'Yan Taliban na ci gaba da kai hare hare a Afghanistan

An kashe Mutane 11 a wani hari da aka kai kan wani gidan saukar baki a babban birnin Afganistan na Kabul

Wani Ba- Amurke na cikin wadanda aka kashe, kuma da dama daga cikinsu na halartar wata liyafa ne a otal din na Park Palace

Jakadan Indiya a Kabul ma ya ce akwai 'yan kasarsa da dama cikin wadanda harin ya shafa

'Yan sanda sun dauki sa'oi biyar kafin su karbe gidan, sannan sun sami nasarar kubutar da mutane fiye da hamsin.

Cikin wadanda suka mutun harda 'yan bindigar biyu, bayan sun kasa tashin bom dinda suke dauke da shi

Babu wata kungiya data dauki alhakin kai harin, amma a 'yan makonnin nan, Kungiyar Taliban ta zafafa hare harenta a Kabul dama wasu wurare a Kasar