Wahala ta sa 'yan gudun hijira shan fitsarinsu

Image caption 'Yan gudun hijirar Rohingya na cikin halin ha'u'la'i.

Kimanin 'yan gudun hijira 'yan kabilar Rohingya na kasar Miyanmar 350 ne suka samu kansu cikin halin ni-'ya-su cikin jirgin ruwa sakamakon rashin ruwa da abinci, al'amarin da ya yi sanadiyar suke shan fitsarinsu.

Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 sun mutu a cikin wannan hali.

'Yan gudun hijirar wadanda suka fito daga wani gari a Miyanmar kusa da kan iyaka da kasar Bangaladash, sun ce kimanin kwanaki shida kenan da matukan jirgin ruwan suka yi ko oho da su.

Hakan dai na faruwa ne sakamakon sabobbin dokokin da gwamnatocin yankin suka samar domin hana fasa kwabrin mutane.

Jirgin yana daya daga cikin jiragen ruwa da dama da suka sami kansu cikin halin ha'u'la'i tun lokacin da kasashen Tailan da Malesiya da Indonesiya suka yanke shawarar dakatar da duk wani jirgin ruwa da ya doshi iyakokin tekunsu.