IS za ta lalata kayan tarihi a Syria

palmyra
Image caption Wani bangaren kayan tarihi a Palmyran Syria.

Shugaban hukumar adana kayan tarihi na kasar Syria ya yi kashedi game da abin da ya kira wata masifa idan `yan bindiga masu ikrarin kafa kasar musulunci a Syria suka karbe iko da garin Palmyra.

Palmyra dai na daya daga cikin yankunan da ke da muhimman kayan tarihi a gabas-ta-tsakiya.

An ruwaito cewa masu ikrarin jihadin sun kame kauyukan da ke kusa da garin na Palmyra, sun kuma kashe mutane fiye da ashirin.

Garin Palmyran dai na daya daga cikin tsofaffin garuruwa a duniya wadanda aka killace, an kuma sanya shi cikin yankuna masu tarihi na duniya karkashin kulawar hukumar UNESCO