'Yan Boko Haram sun sake kama Marte

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption A kwanakin nan dakarun Najeriya kan kwato garuruwan da kungiyar ta Boko Haram ta kama

Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kame garin Marte da ke kan iyaka.

Mataimakin gwamnan jihar, Zannah Umar Mustapha, ya tabbatar da cewa mayakan kungiyar su ne ke rike da gaba dayan garin yanzu, yana mai bayyana hakan da cewa babban koma baya ne ga dakarun Najeriya.

Mataimakin gwamnan ya ce, wasu daga cikin mayakan kungiyar, da dakarun Najeriya ke tarwatsa sansanoninsu a dajin Sambisa, da suka tsere, sun watsu a wasu garuruwa, inda suke shirin kai hare hare.

A ranar Talata da yamma ne mayakan kungiyar ta Boko Haram suka yi wani yunkuri na shiga garin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, amma dakarun Najeriya suka tarwatsa su.

Bayan harin ne hukumomi suka sanya dokar hana zirga-zirga a birnin na Maiduguri, ba dare ba rana.

Sai dai yanzu rundunar sojin kasar ta bakwai da ke Maidugurin, ta bayar da sanarwar sassauta dokar daga karfe takwas na safe zuwa biyar na yamma.