'Yan kungiyar IS sun kwace iko da Ramadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar IS sun kafa tuta a Ramadi

Mayakan kungiyar masu da'awar kafa kasar Muslunci watau IS sun kama hanyar karbe iko da baki dayan birnin Ramadi na kasar Iraki.

Sun yi amfani da hare-haren kunar bakin wake a motoci wajen kutsa kai babban ginin gwamnati.

Bakar tutar masu jihadi a yanzu haka an kafa ta a kan ginin hedikwatar 'yan sanda a birnin yayinda aka yiwa jami'an tsaro kawanya a wani ginin.

Idan har suka kwace wannan muhimmin gari na babban birnin gundumar Anbar, hakan zai kasance babban koma baya ga gwamnatin Iraki.

A waje daya kuma, jami'an gwamnatin Syria sun ce sojin kasar sun sami nasarar fatattakar mayakan kungiyar IS a wani mummunan musayar wuta da suka yi a kusa da birnin Palmyra.

An baiyana fargabar rashin tabbas na muhimman wuraren tarihin dake cikin garin idan ya fada hannun 'yan kungiyar ta IS din.