An sassauta dokar hana fita a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rundunar Tsaro a Najeriya

Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga da ta sanya a birnin Maiduguri a ranar juma'a daga karfe 12 na rana zuwa karfe 5 na yamma.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama'a na runduna ta 7 a Maiduguri Kanal Tukur Gusau ya sanyawa hannu.

Rundunar ta sanya dokar hana fitar ne bayan wani hari da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko haram suka kai a ranar Laraba.

Sojoji dai sun ce sun yi nasarar dakile harin.