Shugaba Nkurunziza ya isa Bujumbura

Image caption Magoya bayan Mr Nkurunziza na murnar dawowarsa

Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza ya koma Bujumbura babban birnin kasar kwana daya bayan da sojojin da ke biyayya a gare shi suka murkushe wani yunkuri na yi masa juyin mulki.

Shugaban ya sami kyakyawar tarba inda magoya bayansa cikin murna, suka yi masa lale marhabun a lokacin da ya isa fadar shugaban kasa tare da rakiyar jerin gwanon motoci.

An kama wani janar din soji da manyan 'yan sanda biyu wadanda ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Sai dai har yanzu ana neman janar Godefroid Niyombare ruwa a jallo wanda shi ne ya jagoranci yunkurin juyin mulkin.

Bayanai sun ce yankin da masu adawa da Mr Nkurunziza su ke, kamar an yi mutu.