'Yan sanda sun kama mutane 145 a Pakistan

'Yan sanda a Pakistan sun ce sun kama mutane 145 a wani samame da suka kai a karachi da nufin gano wadanda suke da hannu a mummunan harin da aka kai kan mota kirar Bas a ranar Laraba.

Ana tunanin cewa wadanda aka kama din sun hada da dalibai guda 90 na wata makarantar Islamiyya.

Har yanzu ba a tabbatar ko mayakan kungiyar IS ko kuma wato kungiyar ce su ka kai harin ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kai hari kan Bas

Mutane 45 mabiya shi'a aka kashe a lokacin da 'yan bindigar suka shiga Bas din suka bude wuta.