Umunna ya janye takarar shugabancin Labour

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Chuka Umunna na da farin jini

Dan majalisar dokokin Biritaniya, Chuka Umunna ya janye daga takarar shugabancin babban jam'iyyar adawa ta Labour.

Mr Umunna mai shekaru 36, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar a shafinsa na Facebook a farkon wannan makon.

Sai dai a wata Sanarwa da ya fitar, Umunna ya ce babu sauki kwata-kwata irin matsin lambar da shugabannin jam'iyya ke fuskanta, shi ya sa ya mayar da wukar.

Mr Umunna wanda ke da farin jini kuma mahaifinsa dan kabilar Ibo ne a Nigeria, an zabe shi ne a karon farko a majalisar dokokin Biritaniya a shekara ta 2010.