Amurka za ta taimaki kasashen Larabawa kare kansu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Barrack Obama

Shugaban Barrack Obama ya ce Amurka tana da babban kuduri na taimaka ma kasashen larabawan ko da zasu fuskanci hari daga wata kasa.

Mista Obama wanda ya sanar da hakan a karshen taronsu da shugabannin kasashen larabawa na yankin Gulf, ya ce Amurka za ta duba yiwuwar amfani da karfi wajen taimakawa kawayenta.

Amurka ta kira taron ne domin kwantar da hankalin kasashen larabawan game da fargabar da suke yi a kan cewa yarjejeniyar nukiliya da Amurka ke shirin kullawa da kasar Iran za ta ba Iran damar kawo rashin zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Kasashen larabawan sun nuna damuwa a game da yiwuwar Iran ta yi amfani da kudaden da za ta samu sakamakon yaye mata takunkumi wajen kunnawa ko rura wutar rikece rikice.

Sai dai a karshen taron, ministan harkokin wajen Saudiya Abdel Al-Jubeir ya ce an ba kasashen larabawan tabbacin cewa manufar yarjejeniyar ita ce a hana Iran mallakan makamin kare dangi.