An sassauta dokar hana zirga-zirga a Maiduguri

Image caption An sasauta dokar takaita zirga-zirga a Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta bakwai dake Maiduguri ta sanar da sassauta dokar takaita zirga-zirga da ta sanya 'yan kwanaki da suka gabata a babban birnin jihar Borno, dake arewa maso gabashin kasar.

An dai sanya dokar ne sakamakon wani yunkurin da wasu 'yan bindiga da ake kautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi na farwa birnin na Maiduguri.

Wata sanarwa da mataimakin mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Kanar Tukur Gusau, ya aike wa da BBC ta ce an sassauta dokar ne sakamakon bunkasar da yanayin tsaro da rundunar ta ce an samu.

Yanzu haka an sassauta dokar ne daga karfe 8:00 na safe zuwa 5:00 na yammaci sabanin yadda yake a 'yan kwanakin da suka gabata, a inda dokar ta takaita zirga-zirga har na tsawon sa'o'i 24.