Bom ya tashi a Damaturu

Bom ya tashi a Damaturu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana zargin yan boko haram da kai hari

Wani Bom ya tashi a Damaturu jihar Yobe a wata tashar mota. Rahotani sun ce wata mace ce 'yar kunar bakin wake ta tayar da bom din a inda ta kashe kanta.

Sai dai babu bayanin yawan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata. Wata majiya tace an killace wurinda da aka kai harin.

Wannan harin yazo a daidai lokacin da sojojin Najeriya ke ikirarin samun nasara akan sansanonin 'yan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno makwabciyar Yobe wadanda ake zargin irin wadannan hare-hare a yankin.