An yankewa Morsi hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mohammed Morsi shine shugaban Misira na farko da aka zaba, sojoji suka hanbarar da shi a 2013

Wata kotu a Misira ta yankewa Morsi tsohon shugaban Misira hukuncin kisa a yau.

Kotun ta yankewa tsoho shugaban kasar hukuncin ne a bisa zarginsa da hannu a balle gidan yari da fursunoni suka yi shekaru da suka wuce.

Lauyan Morsi, Abdel-Moneim Abdel-Maqsoud yace za su dakata su ga matsayin da majalisar shura za ta yanke a watan Juni. Sannan su daukaka kara idan ta amnice da hukuncin kisa

A baya dai wata kotu ta yankewa Morsin hukuncin shekara 25 a bisa zargin azabtar da masu zanga a lokacin da yake mulki.

Mohammed Morsi shine zababben shugaba na farko a Misra, sojoji sun yi mi shi juyin mulki a shekara ta 2013.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na zargin gwamnatin Misira da yin amfani da kotuna don gallazawa Morsi da magoya bayansa.