Boko Haram: Sojoji sun kwato karin sansanoni

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

'Yan Boko Haram da ba a iya tantance yawansu ba sun rasa rayukansu sakamakon luguden wuta da rundunar sojin Najeriya ta yi a sansanonin 'yan kungiyar da kecikin katafaren dajin nan na Sambisa, a ranar Asabar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar, Chris Olukolade, ya fitar ta ce rundunar sojin ta samu nasarar kwato sansanoni har guda 10 daga wurin 'yan kungiyar.

Sannan kuma 'yan kungiyar sun zubar da motoci masu dauke da bindigogin harbo jirgin sama da kuma masu sulke.

Wasu kuma daga cikinsu sun ranta a na kare daga sansanonin nasu suka kuma yi arangama da sojoji a inda sojojin suka samu nasarar kashe su.

To sai dai kuma sanarwar ta kara da cewa 'yan ta'addar sun kai hare-haren kunar bakin-wake a garuruwan Bitta da Kiskeru, to amma fa sojoji sun far musu a kan iyakar Najeriya da Niger kuma ba su ji da dadi ba.