Likita ya manta waya a cikin mara-lafiya

Image caption Likita ya manta wayar salula a cikin wata mata bayan kammala tiyatar haihuwa

A wani asibiti mai zaman kansa da ke Amman a kasar Jordan, wani likitan mata ya manta wayar salula a cikin wata mata bayan da ya yi mata tiyatar haihuwa.

Jim kadan bayan kammala aikin, wadda aka yi wa tiyatar ta fara jin ciwo da zillo a cikinta, abin da yasa mahaifiyarta ta gaggauta daukar ta zuwa wani asibitin gwamnati, a birnin.

An dai dauki hoton cikin a asibitin kuma an gano wani abu a kwance a cikin nata da ba iya tantance wa ba har sai da aka sake fede ta karo na biyu.

Kuma likitocin sun sami nasarar fiddo da wayar salula daga cikin matar.