Dakarun Iraki sun tsere daga Ramadi

Hakkin mallakar hoto AP

Akasarin birnin Ramadi, mai muhimmanci a Iraki, ya fada hannun mayakan kungiyar Islamic State mai da'awar kafa Kasar Musulunci.

Bayan kame tsakiyar birnin da suka yi a ranar Asabar, sun murkushe dakarun gwamnati a ungwannin da ke gefen birnin a ranar Lahadi.

Sai dai wasu rahotanni sun ce har yanzu ana dan samun turjiya a wasu unguwanni wadanda suka ki mika wuya.

Mutane fiye da 500 ne aka kashe a fadan a cikin kwanaki biyun da suka wuce.

Wata 'yar Ramadi da ta tsere daga garin ta bayyana cewa abubuwa sun runcabe sosai.

Ta ce: "Akwai rudani da tarzoma da kuma tashe tashen hankula a ko-ina a kan tituna.

"Bama bamai na fadawa kan mai-uwa-da-wabi a gidaje. Akwai sabbin rahotanni dake cewa an kashe iyalai da dama. Ana ganin mata suna ta gudu akan tituna."

Kungiyar Ismalic State ta yi ikirarin cewa ta samu nasara.

Firaminista Haider al-Abadi ya ce za 'a tura sojin sa-kai 'yan Shi'a domin tinkarar mayakan kungiyar ta Islamic State.

Masu aiko da rahotanni sun ce babbar asara ce ga gwamnatin Iraki ta rasa birnin na Ramadi.

Karin bayani