'Yan kungiyar IS suna shigar burtu zuwa Turai

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan kungiyar IS suna ba-saje da 'yan cirani zuwa nahiyar turai

Wata majiya ta BBC ta samu labarin cewa ana fasakwaurin 'yan kungiyar IS tare da 'yan cirani zuwa nahiyar Turai ta tekun Mediterranean, wato Bahar Rum

Wani mashawarcin karbabbiyar gwamnatin kasar Libya, Abdul Basit Haroun ya ce masu fataucin suna sanya 'yan kungiyar ta IS su saje da 'yan cirani a jiragen ruwa.

Ya ce, tun da farko masu jiragen suna da jerin sunayen mutanen da suke son tafiyar, zuwa Turai, ''amma sun gaya min cewa, wasu mutanen sai su zo da wasu kwatsam, wadanda ba sunayensu a ciki, su umarce su, su tafi da su.''

Wasu masu safarar mutanen a Libya, sun ce masa 'yan IS din suna kyale su, su gudanar da harkokinsu na fasakaurin mutanen, bisa yarjejeniyar ba su kashi hamsin cikin dari na abin da suke samu.