Gwamnatin Katsina na rikici da likitoci

Likitocin Masar din da gwamnatin ta dauko su ne za su tafiyar da sabon asibitin kasa da aka bude a jihar.

Kungiyar likitocin ta Katsina ta ce babu bukatar dauko likitocin daga waje, domin kuwa a gida akwai kwararrun da za su iya tafiyar da asibitin idan za a biya su yadda ya kamata.

Sai dai gwamnatin ta ce ta dauko likitocin ne daga waje domin kara samun ingancin aiki.