An fara raba gidan sauro a Nijar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An fara rabon gidan sauro a Jamhuriyar Nijar.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun fara raba gidan sauro mai magani ga al'ummar kasar domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, wato malaria.

Tuni aka fara raba gidajen sauron a Jihar Maradi bayan da matar shugaban kasar Hajiya Aisata Muhammadu Isufu ta kaddamar da shirin.

Za a raba gidan sauro kimanin miliyan biyu a tsawon kwanaki hudu a jihar ta Maradi.

Sai dai kuma an ce ana samun matsalar turereniya a wuraren da ake karbar gidan sauron.

Ana rabon ne kuma a lokacin da ake allurar rigafin cutar sankarau a jihar.