"'Yan PDP ne suka kayar da jam'iyyar"

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Shugaba Jonathan ya sha kaye a neman tazarce karo na biyu

Sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP Sanata Walid Jibrin, ya ce jagororin jam'iyyar ne da kansu suka yi sanadiyyar kayen da ta sha a zabukan Najeriya da suka gabata.

Sanata Jibrin, shi ne sakataren kwamiti na musamman da jam'iyyar ta kafa domin duba matsalolin da suka sa jam'iyyar ta fadi a zabukan kasar.

Sanata Walid, ya gaya wa wakilin BBC, cewa, sun fadi a zabukan ne saboda kyashi da bakin-ciki da kuma son su cuci 'yan uwansu da suke yi wa junansu a PDP.

Ya ce, saboda haka ne, jam'iyyar ta kafa kwamitin nasu karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Ike Ekweremadu, domin gano wadanda suka yi wa jam'iyyar zagon kasa, a kuma dauki matakan da suka dace a kansu.