Paparoma zai ba Palasdinawa walittaka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Paparoma Francis na rajin kare kiristocin gabas ta tsakiya

Paparoma Francis zai ayyana wasu mata Larabawa masu yi wa addini hidima, wadanda suka rayu a Palasdinu, a lokacin mulkin daular Ottoman ta Turkiyya, a karni na 19, a matsayin waliyyai.

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas, yana birnin Rum domin halartar bikin, wanda wasu Palasdinawan kiristoci su sama da dubu biyu za su halarta ranar Lahadin nan.

Matan dai su ne, Palasdinawa na farko na zamanin nan da za su samu wannan matsayi na walittaka.

Marie Alphonsine Ghattas, wadda ta bude makarantun 'yan mata da kuma Mariam Bawardy, wadda ita kuma ta rika taimaka wa, talakawa, dukkaninsu ana dangantasu da wasu karamomi.

Ana kallon matakin na ayyana su a matsayin waliyyan, da taimako da goyon bayan fadar Paparoma ta Vatican ga tsirarun kiristocin yankin gabas ta tsakiya, da ake ganin suna cikin halin kaka-ni-kayi.