A daina saka 'Janar' a sunana — Buhari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A karshen wannan watan za a rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a Nigeria

Daga ranar 29 ga watan Mayun, 2015, zababben shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce a daina saka 'Janar' a cikin sunansa.

Tsohon shugaban mulkin sojin, ya ce ya fi so da zarar an rantsar da shi a dinga kiransa, Shugaban kasa kuma kwamandan askarawan Nigeria

Darektan yada labarai na yakin neman zaben Buhari, Malam Garba Shehu a cikin wata sanarwa, ya ce shi ma zababben mataimakin shugaban kasa, ya fi son a dinga kiransa Furofesa Yemi Osinbajo SAN.

Buhari ya kasance mutum na biyu da ya bukaci a cire mukamin Janar a sunansa bayan ya samu nasara a zaben shugaban kasa.

Da farko, Janar Olusegun Obasanjo a shekarar 1999, ya bukaci a cire 'Janar' a sunansa, inda ya maye gurbinsa da 'Cif'

Shi kuma mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a wancan lokacin ya bukaci a cire 'Alhaji' daga cikin sunansa idan za a ambace shi.