Boko Haram: shugabanni ECOWAS suna taro a Ghana

Image caption Wasu daga cikin shugabannin kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO

A kasar Ghana, yau Talata ne shugannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS ko kuma CEDEAO za su hallara a birnin Accra don fara babban taronsu karo na 47.

Ana sa ran shugabannin kasashen da za su halarci taron su hada da shugaban Ivory Coast, Alhassan Ouatara da shugaban Gambia, Yaya Jammeh da shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria da shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirlif da kuma mai karbar bakuncin taron wato shugaba John Mahama na Ghana.

Duk da cewa ba bu cikakken bayani kan batutuwan da taron zai mayar da hankali akai, ana hasashen cewa batutuwa kamar nasarar shawo kan cutar Ebola ta addabi kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea.

Sauran batutuwan sun hada da duba ga yanayin tsaro a Najeriya da kuma shirin da yankin yake yi na tura rundunar soji ta-kasa-da-kasa mai kunshe da sojoji dubu 7 zuwa Najeriyar.