Mayakan 'yan Shi'a na kan hanyar zuwa Ramadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan sa-kai 'yan shi'a

Wani jerin motocin mayakan sojin sa kai na 'Yan Shi'a da gwamnatin Iraki ta tura ya isa wani sansanin a kusa da birnin Ramadi wanda ya fada hannun yan gwagwarmayar kasar Musulunci watau IS.

Wani kakakin kungiyar sojin sa kan ta Al-Hashd al-Shaabi ta yan shi'a-- Youssef Al-Kilabi -- ya lashi takobin za su fatattaki kungiyar ta IS daga Ramadi.

Ya ce "Insha Allah za mu samu wannan nasarar, kuma ba za mu amince da duk wani abu da ya gaza haka ba. Za mu kasance kashin bayan dakarun tsaro sannan kuma babbar ganuwar wannan kasa."

Gwamnati dai na fatan rundunar sojin sa kai dubu uku za ta taimaka ga kwato birnin da kuma dakile abin da ta bayyana a matsayin nasara mafi muhimmanci da kungiyar IS ta samu a cikin wani lokaci na kusan shekara.

Mayakan 'yan Shi'a wadanda ke da alaka da Iran a kwanan nan sun taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa dakarun Iraki sake kwato yankuna.